'yan kallo wasa na roba sun maye gurbin 'yan adam a koriya

Image caption Wadanda suka kirkiro su na fatan mutanen na roba za su iya jagorantar kirarin da ake yi a filin wasa.

Wani kulob din wasan kwallon Baseball na kasar Koriya ya fito da wata hanyar karawa 'yan wasansa kwarin gwiwa ta hanyar kawo musu magoya bayan na roba da za su rika zuga su.

Da haka yanzu magoya bayan kungiyar ta Hanwha Eagles za iya sarrafa mutanen na roba idan ba su samu zuwa filin wasa ba.

Mutanen na roba za su iya yin kirari da rera waka da kuma daga hannu ga 'yan wasa- amma ba za su iya shiga cikin filin wasa ba.

Wani kwararre ya ce samar da karin masu goyawa kungiya bayan su halarci filin wasa ta wannan salon na da muhimmanci ga kwararrun kungiyoyi.

''Abin da ya dace ke nan manya kungiyoyin kwallon kafa ke nan su yi'', inji Matt Cutler, editan Sports International a cikin wata hira da BBC.

Image caption Masu sarrafa su kan iya saka fuskocinsu ga fuskar mutum-mutumin.

Amma wani mai kallon wasa John Hemmingham na kallon abin a zaman na ban dariya inda ya ce ''to me zai faru idan dan kallon wasan na roba ya ki yin abin ake son yayi fa, ko ya fusata ko ya yi zagi fa?

Wasu 'yan kallo na kungiyoyi masu hamayya da kungiyar sun kira magoyan bayan nata na roba da kajin Hanwha.

Amma magoya bayanta da ba su samun damar zuwa filin wasa na da zabin tura mutum-mutumin ya wakilce su.

Wasu masu sha'awar wasannin sun yi fatali da kawo mutanen na roba domin ba 'yan wasan Hanwha kwarin gwiwa a zaman wata dabara kawai.

Ba dai abu ne mai sauki ba ga mutum ya zama mai goyon bayan kungiyar Hanwha a Koriya saboda yadda kungiyar ta sha kashi har sau 400 cikin shekaru 5 da suka wuce-abin da ya sa kowa ke tausaya musu.

Karin bayani