Likitan Ebola ya mutu a Saliyo

Dr Umar Khan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dr Umar Khan

A kasar Saliyo, cutar Ebola ta yi ajalin wani likitan da ke jagorantar yakin da annobar cutar a kasar, 'yan kwanaki kadan bayan harbuwarsa da cutar ta Ebola.

Likitan mai suna Sheik Umar Khan ya kamu da cutar ne lokacin da yake jinyar wasu da ke fama da cutar a garin Kenema, garin da ke fama da annobar cutar.

Ministar lafiyar kasar Saliyo, Miatta Kargbo ta jinjina wa marigayin, tana cewa ya isa Gwarzo, lokacin da ta samu labarin cewa ya harbu da cutar.