Ana kara daukar matakan kariyar Ebola a Lagos

Cutar Ebola Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cutar Ebola

Hukumomin lafiya a Nijeriya sun ce sun kebe mutane 59, da ake kyautata zaton sun yi mu'amala da dan kasar Liberiyar nan da ya mutu, sakamakon kamuwa da cutar ebola.

Mutumin ya mutu ne ranar Juma'a a Lagos, bayan da ya isa kasar ta jirgin sama daga Liberiyar.

An kebe mutanen ne a yunkurin tabbatar da cewa ba su harbu da kwayar cutar ta ebola mai saurin yaduwa, wadda kuma ke kisa.

A wata hira da BBC, Dr Nasiru Sani Gwarzo, jami'i a ma'aikatar lafiya ta tarayya ya ce suna daukar matakan da suka dace na ganin sun dakile cutar.