'Niger ce kurar baya a ci gaban al'umma'

Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou

Hukumar kula da ci gaba kasashen ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta fitar rahotonta na wannan shekara kan ci gaban al'umma wanda ya nuna cewa Jamhuriyar Nijar ce ta bayan a kyautatuwar jin dadin jama'a a cikin kasashen duniya.

Rahoton wanda ya saka kasar Norway a zaman ta daya a kyautatuwar rayuwar jama'a, ya ce Nijar ta zo 187 ne a ma'aunin kyautatuwar jin dadin jama'a.

Hukumar ta UNDP dai na amfani ne da bayanan da suka shafi ci gaban tattalin arzikin kasa da kuma irin ci gaban da kasa ta samu ta fannin jin dadin rayuwar al'umarta a bangaren ilmi da kiwon lafiya da samar da ruwan-sha da sauransu, wajen wallafa rahoton nata.

Gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar dai ta ce rahoton bai zo ma ta da mamaki ba, inda ta danganta hakan ka karuwar yawan jama'a.

''Babu al'umma a wata kasar duniya da mata suke yawan haihuwa kamar kasar Nijar, babu inda ake yi ma yara mata aure tun suna kanana kamar Nijar, babu inda ake yi ma yara maza aure tun suna kanana kamar Nijar,'' inji ministan harkokin wajen Nijar din Bazoum Mohammed a wata hira da BBC.