'Ba kuskure a sanarwar ganin watan Sallah'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarkin Musulmi,Mai Alfarma Muhammad Sa'ad Abubakar II

An samu rarrabuwar kawuna a Nigeria game da sanarwar da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta bayar, kan batun ajiye azumin bana da kuma batun yin Sallar idi a ranar Lahadi.

Lamarin ya janyo dubban mutane basu yi amfani da umurnin Sarki Muhammadu Sa'ad ba, inda musamman a kudancin kasar aka yi Sallah a ranar Litinin.

A baya ma an sha samun irin wannan takaddama a kan fara azumi ko ajiye shi a Nigeria.

Fadar Sarkin Musulmi ta ce babu kuskure a sanarwar ganin wata na ranar Sallar Idi.

Farfesa Sambo Wali Junaidu, shugaban kwamitin baiwa Sarkin musulmin shawara ya shaidawa BBC cewar a kan batun ganin wata an samu kuskure tun farko a kan ranar da za a dauki azumin.

Yace " Sanarwar da aka yi ta ranar Lahadi kan batun daukan azumi kuskure ne. Kuma a dage a kan kure ba shi ne daidai ba, sai aka kara fitar da sanarwa a kan cewar ranar da za a soma azumi shi ne Asabar ba wai Lahadi ba."