Boko Haram: Za a kaddamar da gidauniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana dai fatan tara dala miliyan 500 ne nan da watanni 12 domin aiwatar da shirin taimakon.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai kaddamar da gidauniyar tara kudin tallafa wa al'ummomin da hare-haren kungiyar Boko Haram da sauran aiyukan ta'addanci suka dai-shafa a kasar.

Shugaba a ganawar shi da babban sakataren Kungiyar kasahen Commonwealth da kuma shugaban asusun kidaya na Majalisar Dinkin Duniya a Abuja, yayi fatan masu hannu da shuni a kasar da sauran kasahen duniya za su taimaka wajen tara kudin da ake nema.

Karkashin tsarin za a sake gina makarantun da aka lalata da kuma samar da tsaro a makarantun.

A cikin watan Yuli ne gwamnatin kasar ta kaddamar da kwamiti karkashin Theopilus Danjuma don lalubo hanyoyin tara kudi a gidauniyar da kuma duba yadda za a tallafawa mutanen da hare haren suka tagayyara.

Karin bayani