Boko Haram: An cire kwamandoji a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru na shirin kota kwana saboda barazanar Boko Haram

Shugaban Kamaru, Paul Biya ya kori manyan jami'an sojin kasar biyu saboda sace matar wani babban dan siyasa da kuma wasu mutane da ake zargin 'yan Boko Haram sun yi.

Manyan jami'an sojin da aka sallama suna aike ne a lardin arewa mai nisa, inda 'yan Boko Haram ke kai hare-hare, musamman na ranar Lahadi da aka sace matar mataimakin Firaministan kasar.

Tuni aka rantsar da sabbin kwamandojin da suka maye gurbinsu.

Kanal Martin Bayemi shi ne ya maye gurbin Laftanar Kanal Justin Ngonga a matsayin kwamandan sojojin Bataliya ta 34, sai kuma Kanal Pontwoko Peterson wanda ya maye gurbin Gedeon Yossa a matsayin kwamandan daukacin dakarun yankin arewacin kasa.

Kungiyar Boko Haram wacce keda cibiyarta a Nigeria na kaddamar da hare-hare a kan iyakokin kasar inda suke shiga cikin Kamaru musamman ta arewacin kasar.