Ana damuwa kan kaurar Fulani a Kaduna

Image caption Dukkanin bangarorin biyu na fulani da mutanen kudancin Kadunan na dari-dari da juna

A jihar kaduna da ke arewacin Najeriya, ana nuna damuwa a bisa ci gaba da kaurace wa wasu sassa na kudancin jahar da Fulani mazauna da kuma makiyaya ke ci gaba da yi bayan wasu rikice irikice na makiyaya da Manoma a baya.

Shekaru daruruwa dai Fulani suka kwashe suna zaune a kananan hukumomin kudancin jahar kadunan, amma a yanzu da damansu sun kauracewa yankin zuwa wasu sassa na jihohin Pilato, da Benue, da Nassarawa da sauran jihohi na arewa.

Shugabannin fulanin na cewa za su dawo ne kawai idan gwamnatocin kananan hukumomin yankin da ta jiha suka dauki matakan inganta tsaro.