Mutane 33 sun mutu a turmutsutsu a Guinea

Image caption An ayyana zama makoki na kwanaki bakwai a Guinea

Akalla mutane 33 ne suka rasu sannan da dama suka samu raunuka, a wani turmutsutsu, yayin wani shagali na karamar Sallah a Conakry babban birnin kasar Guinea.

Lamarin ya faru ne a wani wurin shakatawa na bakin teku inda dubban jama'a suka je kallon wasan kungiyar wasu fitattun mawakan zamani na Rap.

Kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa turmutsutsun ba.

Kuma hukumomin kasar, sun rufe dukkanin wuraren shakatawa na bakin teku, tare kuma da dakatar da shugaban hukumar da ta shirya bikin.

An kuma ayyana zaman makoki na mako daya a kasar ta Guinea.