Rashin tsaro a kayan gida masu intanet

Image caption HP ba shi ne kamfanin farko da ya gano irin wannan matsala ba.

Kamfanin HP ya gano cewa za a iya kutse a cikin da yawa daga cikin kayayyakin da ke amfani da intanet a gidajen jama'a.

A kan wannan matsalar HP ke ganin ko ya dace a ce irin wadannan kayayyaki na gida sun kunshi muhimman bayanai na sirri na mutum ?

Sashen kula da tsaro na kamfanin na HP ya gudanar da bincike a kan wasu kayayyaki goma da ake amfani da su da intanet.

Wani kwararre kan sha'anin tsaro mai zaman kansa ya ce abin da aka gano abu ne mai tayar da hankali.

Kamfanin na HP bai bayyana sunayen kamfanonin da kayan nasu ke da wannan matsala ba, amma ya nuna kayayyaki goma da ya gudanar da binciken a kansu.

Talabijin mai komai-da-ruwanka da kyamarar jikin kwamfuta da fanfon ban ruwa a lambu da mukullin kofa, da na'urar kuwwa a gida da mabudin garejin mota da sauransu.

Damuwar daya daga cikin wadanda suka yi binciken, ita ce takwas daga cikin kayayyakin da aka yi gwajin a kansu ba sa bukatar mutum ya sa musu lambobin budewa masu sarkakiya ko wahalar ganowa.

Ya ce da dama daga cikinsu ana amfani da lambobi kamar 1234 ko 123456 ne kawai a bude su, kuma a gano bayanan mai amfani da su.

Masana na ganin cewa shin wajibi ne wadannan kayayyaki su tattara bayanan masu amfani da su, kafin su yi aiki ?

A farkon wannan watan, wani kamfanin harkokin tsaro ya bayyana cewa, kwan lantarkin da ke amfani da wi-fi da wani kamfanin Australia, Lifx ya yi, yana bayyana sunan mai amfani da shi da kuma mabudinsa, idan mai kutse ya yi amfani da wata na'ura da ta yi sojan gona kamar wani kwan lantarkin.

A shekarar da ta wuce, sai da kamfanin LG yayi gyara a kan talabijin din kamfanin mai komai-da-ruwanka, bayan da wani mutum ya gano cewa tana nazarin yanayin lokacin da yake kallo, kuma ta yada a intanet karara.