HSBC ya rufe asusun wani masallaci

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption HSBC ya ce babu bambamci tsakanin abokan hudda

Bankin HSBC ya sanar da mahukuntan Masallacin Finsbury Park da wasu kungiyoyin Musulmi da ke Birtaniya a rubuce, cewa zai rufe asusun ajiyar su.

Daya daga cikin dalilan da bankin ya bada na daukar wannan mataki shi ne babu wani shirin ko-ta-kwana da ya yi koda zai samu wata matsala saboda ci gaba da huddar da su.

Bankin ya kuma sanar da wata mata da dan wani mutum da ke tafiyar da wata babbar cibiyar Musulunci a London wannan matakin.

Bankin HSBC ya ce matakin rufe asusun ajiyar kungiyoyin bai da alaka da bambamcin launin fata ko addini.

'Ba bambamci'

''Ba ma tattauna irin dangartakar da muke da ita da abokan huldar mu, kuma ba ma bin kwakwaf na tabbatar da wani ko wata kungiya tana hulda da mu,'' in ji Banki.

''Kyamatar abokan hulda saboda bambamcin launin fata ko addini ba abune mai kyau ba, kuma ba abun amincewa da shi bane. Bankin HSBC yana da shinfidaddun dokoki da ka'idoji na tabbatar da ba a la'akari addini ko launin fata wajen mu'amala da abokan hulda."

A ranar 22 ga watan Yuli ne bankin HSBC ya aika wa Masallacin Finsbury Park takarda a game da rufe asusun ajiyar shi.

Dalilin da aka bayar na rufe asusun shi ne ''a yanzu ci gaba da hulda da masallacin baya cikin wadanda muka yi ma shirin ko ta kwana."

Karin bayani