Gaza: Isra'ila ta kashe 'yan gudun hijira 15

Image caption Iyalan da ke fakewa a cikin makarantar sun kauracewa gidajensu ne domin kaucewa fadan.

Jami'an ma'aikatar Lafiya ta Zirin Gaza sun ce an kashe Falasdinawa 15 wasu kuma da dama suka samu raunukka bayan da tankunan yakin Isra'ila suka harba makaman Igwa kan wata makaranta da Majalisar Dinkin Duniya ta gina.

Wani babban jami'in MDD ya shaidawa BBC cewa an kai ma makarantar hari sau da dama ba tare da an gargadi wadanda ke ciki da su fice ba.

Bob Turner ya ce fiye da falasdinawa dubu uku ne ke fakewa a cikin makarantar sa'adda aka harba mata makaman na igwa da misalin karfe biyar na safiyar Laraba agogon can.

Rundunar sojan isra'ila ta ce tana bincikar lamarin, amma ta ce ta kai hare-hare fiye da ashirin kan wasu hanyoyin karkashin kasa na Hamas.

Karin bayani