'Isra'ila ta kai a hari a wata makaranta'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane 15 sun rasu sakamakon wannan harin a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Isra'ila da kai hari a daya daga cikin makarantunta a Gaza inda dubban Falasdinawa ke samun mafaka.

Kakakin hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza ya ce an kashe yaran ne a lokacin da suke bacci a gefen iyayensu a cikin aji.

Ya bayyana harin a matsayin wani tushen abun kunyar duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana da sheda cewar an harba harsasan ne daga inda dakarun Isra'ila suke.

Hukumar sojin Isra'ila ta ce, sojojinta sun mayar da wuta ne bayan da Falasdinawa 'yan gwagwarmaya suka yi harbi a kansu daga cikin makarantar.

Karin bayani