Boko Haram: Ana Kaddamar da gidauniyar tallafi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yawancin wadanda hare-haren suka rutsa da su dai sun jima suna zargin gwamnatin kasar da rashin taimaka musu.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na kaddamar da gidauniyar tara kudi domin tallafa wa al'ummomin da hare-haren kungiyar Boko Haram da sauran ayyukan ta'addanci ke rutsawa da su ranar Alhamis a fadarsa da ke birnin Abuja.

Mr. Jonathan ya ce kafa gidauniyar wani bangare ne na kokarin da gwamnatinsa ke ci gaba da yi na ganin karshen hare-haren ta'addanci da kasar ke fuskanta da kuma tausayawa wadanda suke rutsawa da su.

''Wadanda abin ke rutsawa da su na bukatar rarrashi da tallafi. Ba za mu iya maido wa jaririn da aka fizge wa rayuwa da rayuwarsa ba, ba za mu iya mai do wa manya maza da mata da aka kashe da rayukansu ba, ba za mu iya mai do da hannuwa da kafafuwan da aka kakkarya yadda suke ba, abin da kawai mu ke iya yi shi ne mu ba su kafadunmu su dafa.'' Inji Shugaban na Najeriya a yayin kaddamar da kwamitin da zai kula da gidauniyar.

Mr. Jonathan dai na fatan mawadatan kasashen da daidaikun jama'a a ciki da wajen kasar za su ba da gudunmuwa ga wannan gidauniyar.

Karin bayani