Za a ba da iznin amfani da motoci marasa matuka a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption A jihar California kawai, wata motar maras matuki ta kamfanin Google ta yi tafiyar mil 300,000 a kan titunan cikin gari.

Gwamnatin Burtaniya za ta dauki wasu matakai na ba da iznin amfani da motoci marasa matuka a kan tituna nan da shekara mai zuwa.

A halin yanzu ana iya amfani da motocin masu tuka kansu ne kawai a titunan harabar gida.

A baya dai Ma'aikatar Sufari ta kasar ta yi alkawalin barin shiga motocin masu tuka kansu a titunan gwamnati a karshen shekarar bara ta 2013.

A watan Disamba, baitil malin kasar ya ce zai samar da gudunmawar kudi Fam miliyan dari daya ga duk gari ko birninda aka fara gwada amfani da motocin a titunansa.

Hakkin mallakar hoto
Image caption A shekarar 2013, kamfanin Nissan ya yi gwajin motar marasa matuki a kan wani babban titi a Japan.

Gwamnatin ta ce tana son nuna cewa Burtaniya ka iya shiga gaba sauran su bi wajen amfani da wannan fasahar, kuma Sakataren Kasuwanci Vince Cable zai sanar da matakan da ake dauka don habbaka bincike kan wannan.

Injiniyoyi a Burtaniyar ciki har da wani ayarin kwararru daga Jami'ar Oxford sun yi ta yin gwaje-gwaje da motocin marasa matuka.

Sai dai damuwa game da batutuwan shara'a da na inshora da ka iya tasowa sun takaita amfani da motocin a titunan harabar gidaje kawai.

Wani kamfanin hada motoci mai suna MIRa ya yi gwajin nasa motocin masu sarrafa kansu a wata farfajiya mai fadin eka 850 a lardin Midlands na Ingila.

Sai dai wasu kasashen sun riga Burtaniya barin motocin su yi tafiya kan titunan cikin gari.

Jihohin California da Nevada da kuma Florida na Amurka duk sun bai wa motocin damar hawa titunan gwamnati.

A jihar California kawai, wata motar maras matuki ta kamfanin Google ta yi tafiyar mil 300,000 a kan titunan cikin gari.

Karin bayani