Bam ya hallaka mutane 10 a Yobe

Hakkin mallakar hoto
Image caption Abubakar Shekau, jagoran Boko Haram

Mutane akalla 10 ne suka rasu sakamakon wasu hare-haren bam da aka kai a wurare biyu a garin Potiskum na jihar Yobe mai fama da rikicin Boko Haram.

Bam din farko an jefa shi ne a cikin Masallacin Alkali Imam Kalli da ke daura da fadar Sarkin Fika lokacin da ake Sallar Isha a ranar Talata.

Mutane biyar ne suka rasu a wurin sannan wasu kusan 30 suka samu raunuka.

Wani da ya shaida lamarin ya gaya wa BBC cewar wani mutum ne a cikin wata mota ya jefa bam din cikin masallacin sannan ya yi gaba da motar.

Hari na biyu kuma wani dan kunar bakin wake ne ya hallaka mutane biyar tare da raunata wasun hudu.

Kawo yanzu jami'an tsaro a jihar Yobe basu ce komai ba game da lamarin.

Kungiyar Boko Haram ta sha kaddamar da hare-hare a jihar Yoben da makwabtan jihohi kamarsu Borno da Adamawa.

Karin bayani