An kashe wani babban limami a China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai dubban Musulmai a China

An kashe limamin Masallaci mafi girma a kasar China wande ke birnin Kashgar a yankin Xinjiang.

Kafar yada labaran gwamnati ta ce mayakan sa-kai musulmi sun daba wa Jume Tahir wuka bayan ya jagoranci Sallar Juma'a a Masallacin Id Kah.

Wakilin BBC a Beijing ya ce babu wanda ya san dalilan kashe Sheikh Jume Tahir wanda dan kabilar Uighur ta marasa rinjaye ne a Xinjiang.

Ya kasance daya daga cikin masu goyon bayan gwamnatin China, abinda ya janyo masa bakin jini a tsakanin 'yan kabilarsa.

Kisan na zuwa ne kwanaki biyu bayan an kashe mutane da dama a wani tashin hankali tsakanin 'yan sanda da wasu matasa a lardin Yarkant.

Karin bayani