Ebola:Saliyo ta kaddamar da dokar ta-baci

Image caption Can tar barke ne a watan Fabarairu a kasar Guinea

An kaddamar da dokar ta-baci a kasar Saliyo a yinkurin shawokan cutar Ebola da ta barke.

Shugaban kasar Ernest Bai Koroma ya ce kawo yanzu an dauki matakan kariya a duka yankunan da cutar tafi illa.

Can ma a kasar Liberia an dauki matakan da suka dace don kaucewa yaduwar cutar.

Kasar Ethiopia ta soma tantance fasinjojin da ke shigowa kasar daga wasu kasashen yammacin Afrika.

A makwabciyar Ethiopia watau Kenya, gwamnati ta sanar da shirin soma tantance duka matafiya ta kan iyakokinta.

Kawo yanzu, cutar ta hallaka mutane fiye da 670 a wasu kasashen yammacin Afrika.

Shugabannin kasashen Liberia da Saliyo sun fasa halartar taron da Amurka ta shiryawa kasashen Afrika a mako mai zuwa domin shawokan cutar ta Ebola.

Karin bayani