'Za mu ci gaba da luguden wuta a Gaza'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gine-gine da Isra'ila ta lalata a Gaza

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce ko da yarjejeniyar dakatar da bude wuta ko babu, Isra'ila ta lashi takobin ganin ta ragargaza dukkanin hanyoyin karkashin kasar da Falasdinawa suka gina domin satar shiga yankunan Isra'ila daga zirin Gaza.

A lokacin da ya ke magana gabanin wani taron ministoci a Tel Aviv, Mr Netanyahu ya ce shi kam ba zai amince da wata yarjejeniya da za ta hana shi ya cimma wannan buri ba.

Jogorar hukumar kare hakkin bil-adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay, ta zargi Isra'ila da bijerewa dokokin kasashen duniya da gangan a farmakin da ta ke kaiwa kan zirin Gaza.

Pillay ta bayyana cewar kamata yayi ya tuhumi Isra'ila da aikata laifukan yaki bayan hare haren da ta kai akan makarantu da asibitoci da gidaje da kuma harabar Majalisar Dinkin Duniya.

Haka nan kuma ta soki lamirin Amurka a kan kasa amfani da fada ajin da ta ke da shi a kan Isra'ila na ta kawo karshen fadan da ma kuma samar da wasu daga cikin manyan manyan makaman da ta ke amfani da su.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Hakkin mallakar hoto BBC World Service