Za mu ci gaba da kai hari a Gaza -Isra'ila

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Isra'ila ta ce za ta nemi afuwa idan ta tabbata cewa makaminta ne ya fada kan makarantar.

Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren soji kan zirin Gaza duk da Allah-wadai da kasashen duniya ke ci gaba da yi da ita kan makaman da ta harba kan wata makaranta ta Majalisar Dinkin Duniya, abin da ya jawo mutuwar Falasdinawa 15.

Sojojin Isra'ilar suka ce farmakin da suke kai ma mayakan Hamas a Gaza zai ci gaba kuma za a fadada shi zuwa wasu sabbin wurare a tsakkiya da kudancin yankin.

Kwamandan sojojin na Isra'ila mai kula da kudanci kasar Janar Sami Turgeman, ya ce sojijin na bukatar wasu kwanakki su gama lalata hanyoyin karkashin kasa da suka gano ya zuwa yanzu.

A nata bangaren kungiyar Hamas ta ce hare-haren Isra'ila na baya-bayan nan kisan-kiyashi ne da ke bukatar martanin mai kama da girgizar kasa.

Fiye da falasdinawa 1,300 ne aka kashe mafi rinjayensu fararen hulla a cikin kwanakki 23 da Isra'ila ta kwashe ta kai hari kan Gaza.

Yayinda aka kashe Isra'ilawa kusan 60, kuma 56 daga cikinsu duk sojoji.

Karin bayani