Ribar Samsung ta ragu da kashi 20% a bana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Karbuwar da wayoyinsa samfurin galaxy suka samu ta Samsung zama kamfanin samar wayar salula mafi girma a duniya.

Ribar da kamfanin kayan latironi na Samsung ke samu ta ragu da kashi 20% a cikin rubu'in wannan shekara na biyu, sakamakon raguwar kasuwar wayoyin komi-da-ruwanka da kuma kara karfi da takardar kudin Koriya ta yi.

Kamfanin dai ya samu ribar Won trillion 6.25 daidai da Fam biliyan 3.6 a cikin rubu'in na biyu; wato tsakanin watannin Yuni da Aprilu, sabanin Won trillion 7.77 da ya ci bara daidai irin wannan lokacin.

Idan dai aka kwatanta da rubu'in farko, ribar ta yi kasa da kashi 17%.

Samsung dai shi ne kamfanin kera wayoyin tafi-da-gidanka mafi girma a duniya, kuma yana samun mafi yawancin ribarsa ne daga sayar da wayoyin.

''Abubuwa da dama ne suka shafi ribar da mu ke samu a cikin wannan rubu'in na biyu cikin har da kwantawar da kasuwar wayoyin komi-da-ruwanka ta yi a duniya da karuwar yawan kudin da ake kashe wa wajen talla,'' inji wata sanarwa da kamfanin ya fitar.

Hakkin mallakar hoto samsung
Image caption Sai dai Samsung na sa ran kasuwarsa ta sake budewa idan ya kaddamar da sabon samfurin wayoyinsa.

A halin da ake cikin kuma kara karfin da takardar kudin Korea ta yi ya shafi ribar da Samsung ya ci cikin wannan lokacin.

Darajar takardar kudin Koriyar wato Won ta tashi da fiye da kashi 11% kan dalar Amurka tsakanin watan Yuli na bara da watan Yunin bana.

Karuwar darajar kudin kan shafi ribar kamfunnan irinsu Samsung- wadanda suka dogara sosai ga aikewa da hajojinsu zuwa kasashen waje- saadda suka aiko da ribar da suka ci a kasuwannin kasashen waje zuwa gida .

Samsung ya ce tashin da darajar takardar kudi ta yi, ta haddasa hasarar Won biliyan 500.

Kamfanin Samsung dai ya bunkasa a cikin 'yan shekarun nan sakamakon ribar da ya samu daga karbuwar da wayoyin salularsa na galaxy suka samu a duniya, abin da ya sa ya sha gaban kamfanin Nokia a zaman kamfanin wayar salula mafi girma a duniya a shekara ta 2012.

Karin bayani