Rikicin kabilanci ya barke a Taraba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Da dama na gannin cewar gwamnati ta gaza shawo kan rikici a Nigeria

Rahotanni daga jihar Taraban Nigeria na cewar wani sabon rikici ya barke a tsakanin 'yan kabilar Jukun da kuma Hausawa a karamar hukumar Ibbi.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai game da musababbin tashin hankalin wanda ya barke a ranar Alhamis da safe.

A baya dai an yi hasarar rayuka da dukiyoyi sakamakon rikicin tsakanin Hausawa da Jukunawa a jihar ta Taraba.

Jihohin Benue da Filato da Kaduna da kuma Nasarawa sun kasance wuraren da ake fuskantar tashin hankali a arewacin kasar.

Nigeria dai na fuskantar kalubalen tsaro a 'yan shekarunan musamman rikici mai nasaba da addinni da kabilanci da kuma matsalar ayyukan 'yan ta'adda musamman a arewa maso gabashin kasar inda 'yan Boko Haram suka hallaka dubban mutane.

Karin bayani