Mutane na kaura daga Buni Yadi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar Boko Haram ta hallaka dubban mutane a Nigeria

Rahotanni daga garin Buni Yadi da ke jihar Yobe a Nijeriya na cewa jama'ar garin suna ta yin kaura zuwa wasu wurare saboda karuwar hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ne ke kai masu, tare da janyewar jami'an tsaro daga garin.

Wani mazaunin garin na Buni Yadi ya fada wa BBC cewa, wannan ita ce kaura mafi girma da mutanen garin suka taba yi.

Yace, "Ba Sarki ba, Chairman, ba Mai unguwa mai dan sanda, babu mai fada a ji a Buni Yadi. Mutane da dama suna ta kaura, wasu basu san inda za su ba."

Al'ummar garin sun ce ba za su koma garin ba har sai gwamnati ta tura musu jami'an tsaro.

Daya daga cikin mutanen garin ya shaidawa BBC cewar 'yan Boko Haram sun aika sako ga al'ummar garin suna umartarsu a kan cewar su bar garin.

Rikicin Boko Haram ya raba dubban mutane daga gidajensu a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Karin bayani