Wani abu ya fashe a ma'aikata a China

Wani mutum da fashewar wani abu ta rutsa da shi a ma'aikatar karafa a China Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akallah mutane sama da dari sun jikkata.

Kafar yada labaran China ta rawaito cewa wani abu mai karar gaske ya fashe a wata ma'aikatar karafa da ke yammacin birnin Kunshan ya hallaka akalla mutane sittin da biyar. Ya yin da kuma wasu fiye da dari suka jikkata a inda ake ayyukan ma'aikatar.

Hotunan da aka wallafa na Internet sun nuna mutane tufafin jikinsu rabi a kone, zazzaune a wajen ma'aikatar, ya yin da bakin hayaki ke tashi daga ciki.

Masu aikin ceto dai na ci gabata da kokarin zakulo wadanda lamarin ya rutsa da su, ya yin da aka fara gudanar da bincike dan gano musabbabin hadrin.

Ana samun yawaitar bala'o'i irin wannan a ma'aikatun kasar China, inda ake korafin rashin maida hankali wajen tabbatar da kariya a ma'aikatun.