Matsalar tattalin arziki a kasar Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekara ta 2013 ce mafi sarkakiya tun bayan rantsar da John Mahama

A 'yan shekarun da suka wuce Ghana na cikin kasashen da suke samun bukasar tattalin arziki.

Sai dai a baya bayan nan tattalin arzikin kasar na samun babban koma baya saboda dimbin bashin da kasashen yammacin duniya suke binta, da yadda darajan kudin kasar watau Cedi yake ci gaba da faduwa.

Hakan na aukuwa ne a lokacin da farashin cocoa da zinare da kasar take sayarwa ke ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya.

Sai dai Shugaban kasar Ghana John Mahama ya ce gwamnatinsa na bakin kokari wajen shawo kan matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

A wata hira da BBC, John Mahama ya ce kuskure ne a danganta halin da kasar ke ciki da koma bayan tattalin arziki.

Karin bayani