Hamas ta musanta sace sojin Israela

Wasu Plasdinawa da luguden wutar Israela ya rutsa da su. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun ranar 8 ga watan Julin da ya gabata Israela ke barin wuta kan zirin Gaza.

Kungiyar mayakan Plasdinawa ta Hamas ta ce ba ta da masaniya game da sojin Israela da ake cewa an kama shi a zirin Gaza.

Hamas ta ce ta yiwu sojan mai suna Hadar Goldin ya mutu ne a fafatawar da aka yi a Gazar.

Plasdinawa dai sun ce an kashe fiye da mutane casa'in a sabon harin da Israela ta kaddamar sa'o'i kadan bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'i 72 a jiya juma'a.

Shugaba Obama yace zai yi kokarin ganin an sake wata yarjejeniyar, ya kuma kara da cewa abin a tausaya ne ga halin da fararen hula ke ciki a Gaza.

Ya kuma kara da cewa ya yi Allawadai da kisan sojojin Israela biyu da Hamas da Plasdinawa suka yi, da kuma satar soji na 3.

Mr Obama ya ce idan har Hamas da gaske take dan kawo karshen rikicin da ake yi ya zama dole ta sako sojan nan cikin gaggawa.