Gaza:Yarjejeniya tsagaita wuta ta wargaje

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane sun rasa muhallansu

Wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta kwanaki ukku ta wargaje 'yan sa'o'i kadan da fara aikinta, inda Isra'ila da Falasdinawa kowanensu na zargin juna da keta yarjejeniyar.

Jami'ai a zirin Gaza sun ce bindigogin atilari sun hallaka mutane akalla 35 kuma sun jikkata wasu 100 a kusa da garin Rafah da ke kudancin zirin Gazar.

Jami'an Isra'ila sun ce sun dauki wannan mataki ne domin maida martani a kan hare-haren da Falasdinawa suka kai da rokoki.

Najwa Taher, wata dake zaune a sansanin 'yan gudun hijira ta bayyana takaicin da ta ji da ta samu labarin yarjejeniyar dakatar da bude wutar ta wargaje.

Tace "Ina sauraren wani gidan radiyo ne 'yan mintina kadan da suka wuce sai suka bada sanarwa da harshen yahudanci cewar yarjejeniyar ta wargaje. Wannan babban abun tsoro ne, saboda da mun yi tsammanin komai zai dai-dai ta."

Karin bayani