Mutum-mutumi ya yi tafiya da karyayyar kafa

Mutum-mutumi da karyayyar kafa
Image caption Mutum-mutumi da karyayyar kafa

Injiniyoyi sun kara samun cigaba wajen samun injuna da za su cigaba da aiki ko da kuwa sun samu lahani ta hanyar kera wani mutum-mutumi wanda ya koya ma kansa tafiya duk da kafar sa guda ta karye.

Yayinda suka yi wani gwaji, wani mutum-mutumi da suka yi mai kafa shida, ya sake koyon tafiya cikin kasa da minti biyu.

Injiyoyin suka ce, sabuwar dabarar za ta sanya a samar da mutum-mutumi mai amfani kuma wanda zai iya zaman kansa.

Suka ce manufar yin haka don a kwaikwayi dabbobi ne wadanda suke da rauni.

Wannan hanya ta gwaji za ta yi tasiri ga mutum-mutumin da ake amfani da su a wuraren aiki da kuma dalilai na aikin soji. Mutum-mutumi zai cigaba da kai hari - ko ma wane irin lahani ya samu idan aka dubi yadda abinda mutum-mutumi na android ke yi a fina-finai na Terminator.

A cewar wani kwararre, mutum-mutumin da za su saje da yanayi, cigaba ne a fagen fasaha. Yawancin mutum-mutumi a yanzu, a masana'antu suke kuma suna wasu ayyuka ne kebabu. Masana kimiyya suna so, su mayar da mutum-mutumin ya zamanto yana fahimtar sabo da sauyin yanayi.

Dr Fumiya Lida na Jami'ar Cambridge ya ce, akwai ayyuka da suka zarce na soji kamar mutum-mutumin dake duniyar Wata ko Mars.

"kalubale na hakika da muke fuskanta wajen kera mutum-mutumi shine na yadda za a samar da mutum-mutumin da zai iya sajewa da yanayi ko ma wane iri ne," Dr Fumiya Lida din na jami'ar Cambridge ya sheida ma BBC.

"lokacinda dabbobi suka ji rauni a kafar su, sukan koyi yadda za su yi tafiya da sauran kafafuwan" a cewar masana a wani bincike. To amma lokacinda mutum-mutumi suka samu wani lahani a kafa, sai su zamo ba su da wani amfani."

Masana kimiyyar suka ce, a yanzu an kago hanyar da mutum-mutumin zai warware wannan matsalar ta hanyar kwaikwayon dabbobi wajen gane kowacce kafa ce ta karye, daga nan sai ya yi kokarin hanyar da zai yi cigaba da tafiya.

Karin bayani