Emirates ya dakatar da zirga zirga a Guinea

Jirgin saman Emirates Hakkin mallakar hoto a
Image caption Jirgin saman Emirates

Kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Emirates ya dakatar da jigilar jiragensa zuwa kasar Guinea har sai abin da hali ya yi saboda barkewar cutar Ebola.

Cutar ta Ebola dai ta hallaka mutane 700 a yammacin Afirka a bana.

A cikin wata sanarwa a shafinsa na yanar gizo kamfanin yace ba zai yi sake da lafiyar fasinjojinsa da kuma ma'aikata ba.

Haka ma dai wasu kamfanonin zirga zirgar jiragen sama na Afirka guda biyu Arik Air na Najeriya da kuma ASKY na kasar Togo su ma sun dakatar da zirga zirgar jiragensu zuwa kasashen da cutar ta bulla.

A ranar Juma'a babbar daraktar kungiyar lafiya ta duniya Margaret Chan ta ce kwayar cutar Ebola na yaduwa da gaggawa fiye da yadda ake kokari wajen shawo kanta.

Karin bayani