Isra'ila ta cigaba da kai farmaki a Gaza

Wani gini da aka yiwa luguden wuta a Rafah Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luguden wuta mafi muni ya faru ne a Rafah

Hukumomin lafiya a zirin Gaza sun ce Falasdinawa 200 ne suka hallaka a luguden makamai masu linzami da Isra'ila ta harba tun bayan rugujewar takaitacciyar 'yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Juma'a.

Luguden wuta mafi muni ya faru ne a Rafah inda Israi'la ta yi amannar mayakan Hamas sun sace wani sojanta guda.

'Yan gwagwarmayar Falasdinawan su ma sun harba rokoki zuwa cikin Israi'la.

Hamas dai ta zargi Isra'ila da keta sharuddan 'yarjejeniyar, amma rundinar sojan Isra'ila ta ce ya zame ma ta dole ne ta maida martani ga hare-haren roka da Falasdinawa ke kai ma ta.

A halin da ake ciki kuma, ana cigaba da kokarin sulhunta rikicin a Masar inda wata tawagar Palasdinawa ta isa birnin Al -Kahira, amma Isra'ila ta tabbatar cewa ba za ta tura wakilanta wajen tattaunawar ba.

Shugaban Masar din Abdul Fatah al -Sisi ya dage kan cewa shirin tsagaita bude wuta da kasarsa ta gabatar, wata muhimmiyar dama ce ta kawo karshen zubar da jinin da ake yi.

Karin bayani