'Yan bindiga sun kashe Hakimin Soro

Hari a Bauchi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hari a Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi a arewacin Nijeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun bindige wani basaraken gargajiya da kanensa har lahira a karamar hukumar Ganjuwa.

Sun kuma kashe wani dan kasuwa.

Lamarin ya faru ne jiya da dare a garin Soro, kuma 'yan bindigar sun sulale bayan da suka aikata kashe-kashen.

Wani mutum da ya sheida lamarin ya ce garin ya rude da harbe-harben bindigogi a lokacinda ake kai harin.

'Yan sandan jihar Bauchi sun tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yanzu haka suna cigaba da sintiri a garin.

Karin bayani