Gidauniya, a sanya talakkawan cikin rabo

Wadanda harin boko haram ya shafa
Image caption Wadanda harin boko haram ya shafa

A Najeriya wasu 'yan majalisar dokokin kasar dake wakilartar wasu yankuna da hare-haren kungiyar Boko Haram suka daidaita sun soma tofa albarkacin bakinsu game da gidauniyar da Shugaban Najeriyar ya kaddamar.

Wadda ke neman kudaden da za'a kashewa wadanda hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram din ya shafa musamman a yankin arewa maso gabashin Kasar.

Dala miliyan dari biyar dai gwamnatin Najeriyar take sa ran tattarawa domin wannan manufa cikin shekara guda.

'Yan majalisar dake tofa albarkacin bakin na su, sun ce lallai ne sai an hada hannu da mutanen yankin karkara wajen rabon taimakon nan, domin su ne suka san matsalolin kan su.

Karin bayani