Niger: Hukumomi sun hana taron MNSD

Seini Oumaru shugaban MNSD Nassara Hakkin mallakar hoto
Image caption Seini Oumaru shugaban MNSD Nassara

Wata yarinya ta rasa ranta bayan da jami'an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa wani taron 'yan adawa na jma'iyyar MNSD Nasara a birnin Damagaram.

Yan adawar sun ce wasu karin mutane da dama sun sami raunuka kuma an yi awon gaba da wasu mutanensu.

Hukumomin birnin na Damagaram dai sun ce sun dauki matakin ne saboda ba su ba 'yan adawar izinin gudanar da taron ba.

Amma 'yan adawar sun ce wata kotu a birnin Yamai ta ba su izin yin taron nasu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da hukumomi ke hana 'yan adawa gudanar da taronsu a Damagaram ba.

Karin bayani