An kori babban daraktan Vkontakte a Rasha

Shugaba Putin a taron masu internet a Rasha Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Putin a taron masu internet a Rasha

Wanda ya kirkiro shahararren shafin nan na sada zumunta na Rasha ya ce an kore shi daga aiki, kuma aminnan Shugaba Putin sun karbe iko da shafin na sa.

Pavel Durov, wanda ke tafiyar da shafin mai suna Vkontakte, a can baya ya bayar da sanarwa cewar zai bar kamfanin, to amma yace ya janye niyyar sa ta yin murabus.

Kamfanin dai ya musanta cewar Mr Durov ya janye aniyar ta sa.

Mr Durov, a can baya, ya ki yarda da bukatar gwamnatin Rasha wadda ta nemi ya rinka tace labaran da ake aikawa a shafin na sa.

A cikin wata sanarwa, Mr Durov ya ce bai san da labarin korar ta sa ba, sai a kafofin watsa labarai. "yace, a yau, an kore ni daga matsayi na, na babban daraktan kamfanin Vkontakte." Yace, abin sha'awa ne da masu hannun jari a kamfanin ba su dauki matakin nan ba kai tsaye, don haka ne na samu labarin ta kafofin watsa labarai.

"A yau, kamfanin Vkontakte ya koma karkashin kulawar Igor Sechin da Alisher Usmanov. Mai yiwuwa, a tsarin Rasha, wani abu irin wannan, ba shi da makawa, to amma ina farin ciki, mun kwashe tsawon shekaru bakwai da rabi tare. Mun yi aiki tukuru. Abinda kuma muka yi, ba za a taba wargaza shi ba."

Mr Sechin shine babban jami'i na kamfanin man feturi mallakar kasar watau Rosneft kuma tsohon mataimakin babban jami'i na ma'ikatan Mr Putin.

Mr Usmanov wanda a cewar Forbes, shine mutumin da ya fi kowa kudi a Rasha, ya samu kudin sa ne ta ma'adinin tama da karafa, kuma kafin wannan lokacin yana da hannun jari a shafin sada zumunta na Facebook. Yana da hannun jari mai karfi a kamfanin Vkontakte ta hannun kamfaninsa na internet Mail.ru.

Mr Durov, ya ba da sanarwar murabus din sa a bainar jama'a a ranar 1 ga watan Aprilu, to amma kwanaki biyu daga bisani yace, irin wasan nan ne na April fool.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha interfax ya ba da rahoton cewa kamfanin sada zumuntar na Vkontakte ya ce ya dauki matakin ne ta aiki da wasikar ajiye aikin da Mr Durov ya rubuta a ranar 21 ga watan Maris tunda bai janye ta ba a hukumance a cikin wata daya da aka tsara mutum zai iya janyewa.

Karin bayani