Ebola: Amurka za ta taimakawa Afirka

Yaki da cutar Ebola Hakkin mallakar hoto ebola
Image caption Yaki da cutar Ebola

Wani babban jami'in lafiya na Amurka yace Amurkar za ta tura jami'an kiwon lafiya akalla hamsin zuwa yammacin Afirka nan da wata daya domin taimakawa wajen shawo kan annobar Ebola mafi muni da ta barke.

Thomas Frieden daraktan cibiyar kare cutattuka masu yaduwa yace a yanzu cutar ta Ebola ta na nema ta gagari kundila sai dai yace ana iya tsayar da ita ta hanyar matakan lafiya daga tushe.

Yace cibiyar kare cutattuka masu yaduwa ta dukufa wajen habaka matakan martani ga cutar.

Jami'in yace Amurka za ta tura kwararrun jami'an kiwon lafiya akalla hamsin zuwa kasashe uku da cutar ta bulla wadanda suka hada da Guinea da Liberia da kuma Saliyo nan da kwanaki talatin masu zuwa.

Cutar ta Ebola dai ta hallaka mutane fiye da 700 ya zuwa yanzu a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo.

Karin bayani