An hana a kwace shafin Internet na Iran

 Kungiyoyin da ake zargi da ta'addanci a Iran Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyoyin da ake zargi da ta'addanci a Iran

Hukumar dake sa ido ga shafukkan Internet ta duniya ICANN ta yi kira ga wata Kotun Amurka ta dakatar da yunkurin kwace shafin Internet na kasashen Iran, Syria da Korea ta Arewa.

Iyalan mutanen da ayyukan ta'addanci suka takaita ne ke yunkurin kwace shafin na .Ir,.sy da .Kp.

Da za ran aka kwace shi, za a rinka amfani da shi ne don neman diyya ga mutanen da ayyukan ta'addancin suka shafa - wadanda tuni an rigaya an biya su diyyar hasarar da suka yi a wata shari'a da aka yi a wata Kotun Amurka tun kimanin shekaru goma da suka wuce.

A karar da ta shigar, hukumar dake sa idon kan shafukkan na Internet ICANN ta ce, muddin aka kwace shafin, to zai zamo ba shi da wani amfani, don haka babu wata diyya da za a samu.

Yunkurin kwace shafukkan wani bangare ne na shari'ar da ake yi a wata Kotu da iyalai hudu na wasu Amurkawa suka shigar wadanda aka raunata a wani harin kunar bakin-wake da aka kai birnin Kudus a shekarar 1997 wanda kungiyar Hamas ta dauki alhakin kai wa.

Iyalan sun kai karar kasar ta Iran ne saboda goyon bayan ta ga Hamas tare da neman diyya ga raunukan da iyalansu suka samu ta hannun kotuna.

Kungiyar mutanen dai ta yi nasara sakamakon rashin zuwan kasar ta Iran kotu ta kare kan ta, don haka ne a shekara ta 2003 aka baiwa kungiyar dola 109 a matsayin diyya. Tun a shekarar ta 2003, kungiyar mutanen ke ta kokarin mamayar kadarorin kasar Iran wadanda ta san suna Amurka a kokarin karbar wadannan kudade.

A shekaru goman da suka wuce, sun samu nasara ta wasu fannoni, yukurin kwace shafin Internet din ne na Iran ke jerin abubuwa na karshe da kungiyar ta shirya. Ba a dai tantance kowanne dalili ne ya sa kungiyar ke kumajin kwace shafukkan na Internet na kasashen Syria da Korea ta Arewa.

Doriyar karshe an san ita ce ke kasancewa tsarin babban shafin kasa, kuma kowacce kasa ta duniya tana da daya wanda a kansa ne kowanne shafin internet ya jingina.

Hukumar dake sa ido ga shafukkan Internet din ta duniya ta shigar da kara a wata Kotun dake Columbia tana neman a yi watsi da bukatar kungiyar ta kwace shafukkan na Internet na kasar ta Iran, duk da yake dai ta nuna juyayi ga koken da kungiyar ta gabatar.

Karin bayani