Nijar na bukukuwan samun 'yancin kai

Mahamadou Issoufou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahamadou Issoufou, Shugaban Nijar

Jama'a a kasra Nijar, na bukukuwan cika shekaru hamsin-da-hudu da samun 'yancin kai.

Shugaban kasar, ya yi wa 'yan kasar wani jawabi a yayin bikin, inda ya ce gwamnatinsa zata maida hankali sosai akan maganar tsaro.

Shugaban ya kuma yi amfani da bikin wajen jaddada cewa Nijar zata ci gaba da hada kai da kasashen yammacin duniya don tabbatar da tsaro a yankin sahel.

Ya kuma zayyana wasu nasarorinda ya ce gwamnatin sa ta samu

Sai dai wasu masu fashin baki a kasar na ganin cewa har yanzu akwai jan aiki a gaban mahukuntan kasar wajen inganta rayuwar talakawa.

Dokta Youssofou Yahaya, wani malamin jami'a a kasar ya shaidawa BBC cewa: "Dan kasa shi ya kamata ya ce yaji dadi wuri kaza," ba wai gwamnati tace tayi aiki kaza ba.

Nijar dai na fuskantar kalubalenda suka hada da karancin abinci da kuma tsaro.

A shekarar 1960 kasar ta samu 'yancin kai daga turawan Faransa da suka mulke ta.