An keta hakin bil'adama a Najeriya

Kungiyar Amnesty International Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyar Amnesty International

Kungiyar kare hakin bil 'adama ta Amnesty International ta ce ta bankado bayanai da suka nuna cewar an aikata laifukan yaki a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar na zargi sojojin Najeriya da kuma 'yan kungiyar Boko Haram da keta hakin bil'adama.

Kungiyar ta ce ta samu wani bidiyo da ya nuna wasu mutane da ake zargin sojojin Najeriya ne da kuma 'yan kato da gora na yanka wuyar mutanen da suka kama.

Ta kuma zargi Boko Haram da aikata miyagun laifuka .

Kungiyar ta Amnesty International ta nemi a gudanar da bincike akan abin da ta kira yawaitar keta hakin bil'adama daga wurin bangarorin biyu.

Kungiyar ta kammala rahoton ne bayan ziyara da ta kai jahar Borno inda ta yi amfani da hotunan bidiyon da ta samu daga bangarori daban daban.