Wani likita ya kamu da Ebola a Nigeria

Likita na gwaji a asibiti a Najeriya
Image caption Wani jami'in lafiya a dakin bincike a Nigeria

Hukumomi a Najeriya sun ce likitan da ya duba dan kasar Liberiyan nan mai dauke da cutar Ebola a jihar Lagos ya kamu da cutar.

Hakan na nufin shi ne mutum na biyu da aka tabbatar ya kamu cutar a Legas, wanda shi ne birni mafi yawan mutane a yammacin Afrika.

Ministan lafiya Onyebuchi Chukwu, wanda ya tabbatar da likitan na dauke da cutar, ya ce ana can ana yi masa magani, kuma a yanzu mutane 70 da aka yi amannar cewa sun yi mu'amala da dan kasar Liberiyar, ana kula da su inda takwas daga cikinsu aka kebe su.

An kuma dauki jinin karin wasu uku da alamu suka nuna suna dauke da cutar, domin yin gwaji.

Karin bayani