Facebook zai fadada harkokinsa a Afrika.

Kamfanin Sada zumunta Facebook Hakkin mallakar hoto
Image caption Kamfanin Sada zumunta Facebook

Wannan wata sabuwar iyaka ce ga hanyar sadarwa ta zamani watau Internet - hada miliyoyin mutane a Afrika da Asia wadanda har yanzu ba su bude ido ba da muhimmancin dake tattare da cigaban zamani ta hanyar kimiyya da fasaha.

Ta hanyar wani kamfani da ake kira Internet.org, kamfanin sada zumunta na Facebook ya ja ragama ga kokarin cimma wannan manufa.

A yau, kamfanin ya sanar da wani shiri na fasaha na hada miliyoyin mutane a Zambia da hanyar sadarwa ta zamani.

Babu ko shakka wannan yunkuri na taimaka ma mutane - kuma a karshe zai zamo abu mai matukar muhimmanci ga habakar kamfanin sada zumunta na Faceboook.

Kamar yadda Guy Rosen na Internet.org ya bayyana mi ni a kan wani hadi na Video daga hedkwatar Facebook dake Menlo Park, kashi 85 cikin dari na mutane wadanda ba a hada su da hanyar sadarwa ta Internet ba suna wurare ne da wayoyin salula ke kaiwa.

Akwai dalilai biyu da suka sa haka, duk da yake ana yawan amfani da wayoyin na salula, ba su gwada hanyar sadanwar ta Internet ba - mutane ba su da karfi da rashin sani. Idan ba haka ba, kudin da ake kashewa a wayoyin salula suna da yawa idan aka kwatanta da internet, kuma mutane da dama ba su da masaniyar alfanun da za ta yi musu.

Shirin da za a yi a Zambia duk zai magance wadannan matsalolin. Kamfanin sadarwa na wayar salula Airtel - kamar wasu a Afrika yana ba da kafar shiga shafin sada zumunta na Facebook kyauta a wayoyin salula.

Yanzu a Zambia, kamfanin zai ba da damar shiga Internet.org wanda ta hanyarsa za a iya shiga shafin Facebook da sauran wasu shafukkan na Internet. Masu wayoyin na salula za su iya shiga Wikepedia, da Job sites watau shafukkan neman aikin yi, da yanayi da bayanai a kan kiwon lafiya kuma duk a kyauta ba tare da biyan karin wasu kudade ba.

Masu wayoyin salula za su iya shiga wadannan shafuka daga 'yar karamar wayar da suke da ita ta hanyar shiga shafin Internet.org, za a kuma gargade su, idan suka nemi shiga wasu shafukka wadanda ake cajin kudi.

Kashi 15 cikin dari ne na mutanen Zambia miliyan 15 ke amfani da hanyar sadarwa ta Internet kawo yanzu - fatar da ake yi a yanzu ita ce, mutane da dama za su yi kokarin gwada wannan hanya. Idan kuma wannan gwaji ya yi nasara, za a iya amfani da irin wannan dabarar da sauran wasu kamfanonin na Salula a sauran wasu sassa na Afrika.

Karin bayani