An tsagaita Bude wuta a Gaza

Gaza resident Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani da ya samu rauni a harin da Israela ta kai a Gaza

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza na tsawon sa'o'i bakwai na ci gaba da kasancewa.

Amma yarjejeniyar ta takaita ne ga wasu yankuna na zirin Gazan.

Wani babban jami'i na sojojin Israela ya ce tsagaita wutar bai shafi yankunan Rafah da ke kudanci ba, kuma Israela na iya mayar da martani da zarar an kai mata hari.

Matakin tsagaita bude wutar Israelan na zuwa ne kwana daya bayan Majalisar Dinkin Duniya ta soki Israela a kan harin da ta kai kusa da wata makaranta da ke karkashin kulawar Majalisar, inda mutane akalla goma suka rasa rayukansu.

Karin bayani