Microsoft zai kai Samsung kara

Kamfanin Microsoft zai kai kamfanin Samsung kara a gaban kotu game da zargin bashin da ya ke binsa wajen amfani da fasaharsa ta Android.

Microsoft ya ce Kamfanin Samsung na kasar Koriya ta Kudu ya gaza biyansa kudi akan lokaci kuma ya soma shirye shiryen shigar da kara a gaban kotu a birnin Newyork.

A cikin shafinsa na internet kamfanin Microsoft ya ce Samsung na fakewa da sashin wayoyin tafi da gidanka na Nokia da Microsoft ya saya a matsayin dalilin da ya sa be cika alkawarinsa ba.

Sai dai Samsung ya ce zai yi nazari kan korafe korafen tare kuma da daukar matakan da suka dace.

Hakkin mallakar hoto AP

Wannan shi ne karon farko da kamfanin Microsoft zai dauki matakin shigar da kara a gaban kotu bisa zargin kamfanin Samsung da aikata ba dai -dai.

Kamfanonin biyu sun kula kawance , saboda kyumfuta ta Windows PCs da kuma wayoyin da Samsung ke samarwa.

Samsung ya amince ya biya Microsoft kudi a shekarar 2011 sai dai takardun da lauyan Microsoft ya wallafa a shafin internet sun nuna cewa Samsung ya dakatar da biyan kaso na biyu na kudin bayan ya samu labarin yarjejeniyar kasuwanci da aka kula tsakanin Microsoft da Nokia.

Hakkin mallakar hoto AFP

Sai dai Microsoft be ji dadin shawarar da Samsung ya yanke ba na kin biyan sauran kudin.

Takardun sun nuna cewa Samsung ya yi ikirarin cewa Microsoft ya sabawa kaidojin amfanin da fasahar juna sakamakon kamfanin Nokia da ya saya.

Sai dai Samsung be ce uffan game da zargin ba.

Microsoft be ta ba bayana yawan kudin da ya ke samu daga fasaharsa da yake bayar wa haya ba , kodayake masu sharhi sun yi kiyasin cewa kudin ya kai dala biliyan daya zuwa dala biliyan biyu a kowace shekara