Sudan ta Kudu na gab da fadawa cikin yunwa

Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu matuka akan yadda al'amaura ke tababbarewa a garin Bunj dake kasar Afrika ta Kudu.

Ta ce an kashe wani ma'aikacin agaji jiya litinin , kuma an yi artabu tsakanin mayakan sa kai da kuma sojoji da suka tsere da ke zargin suna alaka da 'yan tawaye.

Wani ma'aikacin agaji ya shaidawa BBC cewa dubun dubatar mutane sun tsere zuwa zuwa sansanoni dake samar da mafaka ga 'yan gudun hijira daga makwabciya Sudan.

Ana cigaba da fada yayinda gwamnati da kuma 'yan tawaye suka koma akan teburin shawara a kasar Ethiopia.

Mutane fiye da abin miliyan suka rasa muhalinsu a yakin.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi gargadin cewa kasar Sudan ta Kudu na gab da fadawa cikin yunwa.