Ebola: Bankin duniya ya bayar da dala miliyan 200

Shugaban bankin duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jim Yong Jim, shugaban bankin duniya

Bankin duniya ya bayar da taimakon gaggawa na dala miliyan 200 ga kasashen yammacin Afrika uku, na, Sierra Leone da Liberia da kuma Guinea, wadanda ke fama da annobar cutar Ebola, domin yaki da ita.

Shugaban bankin, Jim Yong Kim, ya ce, ya damu matuka kan yadda cutar ta Ebola ta daidaita, fannin kula da lafiya na kasashen, wanda dama mai rauni ne.

Mr Kim ya ce za a yi amfani da wannan kudi ne domin samar da muhimman kayayyakin kula da lafiya da kula da ma'aikatan lafiya, a kuma taimaka wa mutanen da annobar ta jefa cikin wani mawuyacin hali.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta hallaka mutane kusan 890 a yankin na Yammacin Afrika.