Taron gaggawa akan cutar Ebola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kimanin mutane 900 ne suka hallaka sakamakon kamuwa da cutar Ebola a Yammacin Afrika

Hukumar lafiya ta duniya WHO na wani taron gaggawa domin lalubo hanyar da za a shawo kan annobar cutar Ebola a Yammacin Afrika.

Ana saran kwararru za su yanke shawara zuwa ranar Alhamis, ko za a ayyana matakin dokar ta baci, wanda zai iya hadawa da sanya matakin hana tafiye-tafiye zuwa kasashen da cutar ta shafa.

Annobar dai ita ce mafi muni da aka taba gani, inda ta hallaka mutane kusan 900.

A farkon shekaran nan cutar ta fara bazuwa a Guinea inda ta yadu a wasu kasashen Yammacin Afrika uku, Liberia da Saliyo.

A baya bayan nan an samu wasu mutane 'yan kalilan da suka harbu da kwayar cutar a Najeriya.