Palasdinawa sun fara komawa gida a Gaza

Wasu yara a Gaza Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu yara a Gaza

Duban Palasdinawa ne a Gaza ke ci gaba da komawa gidajensu daga sansanin 'yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya, bayan da yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 3 tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta fara kankama.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, ta janye dakarunta, tare da bayyana cewa bukatarta ta lalata hanyoyin karkashin kasa daga Gaza ta biya.

Amma kuma kungiyar Hamas ta bayyana farmakin da Isra'ila ke kaiwa a matsayin faduwar bakar tasa dari bisa dari.

Yayinda yake magana daga birnin Qatar, babban mai magana da yawun kungiyar Hamas Osama Hamdan ya shaidawa BBC cewa zaman tattaunawar da za a yi tsakanin bangarorin biyu a Masar wata dama ce da Isra'ila za ta samu ta nuna dattaku.

Masar ce dai ta shirya dakatar da wutar, inda Israila ta ce ta amince da yarjejeniyar ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Jami'ai a Gaza sun ce an kashe Falasdinawa 1,800, yayin da Israila kuma ta rasa sojoji 67 a makonni hudu da aka kwashe ana yakin.

"Dakarun Isra'ila za su koma wajen Zirin Gaza inda za su tsaya domin kare duk wani yunkuri na kai hari" a cewar kakain rundunar laftanal kanal, Peter Lerner.

A nata bangaren, ita ma Hamas, ta yi alkawarin mutunta yarjejeniyar.

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka, sun yi marhabin da matsayar da aka cimma, tare da fatan bangarorin biyu za su mutunta ta.

Karin bayani