Mazauna garin Ibi na cikin mawuyacin hali

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Fadan ya barke ne tsakanin kabilar Jukun da Hausawa da kuma Fulani

Rahotanni daga jihar Taraba a arewacin Nigeria na cewa jama'ar garin Ibi na cikin wani mawuyacin hali, yayin da suka shiga yini na shida a karkashin dokar hana fita ba-dare-ba-rana.

Mazauna garin dai na kukan rashin damar samun kayayyakin masarufi, ga rashin lafiya, kuma ba sa iya fita domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Yayin da wasu bayanai ke nuna cewa jami'an tsaro sun bindige wani farar hula, kana suka jikkata wani daban, a lokacin da suka yi yunkurin fita daga gidajensu.

Tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne aka kafa dokar hana fitar a garin na Ibi, bayan wani tashin hankali a makon jiya wanda ya yi sandiyyar mutuwar mtane da dama.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba