Gaza: Kerry ya nemi a fadada yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption John Kerry ya kara dora alhakin hare haren Gaza a kan Hamas

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya nemi Isra'ela da Palasdinu su yi amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma wajen fadada tattaunawar zaman lafiya a tsakaninsu.

A wata hira da ya yi da BBC, Mista Kerry, ya ce akwai bukatar bangarorin biyu su mayar da hankalinsu wajen tabbatar da kafuwar kasashensu biyu.

Kerry ya kara da cewa Isra'ela na da 'yancin kare kanta daga hare haren rokoki da Palasdinawa ke kai mata, sannan kuma ya dora laifin hare haren a kan Hamas.