LinkedIn zai biya diyyar dala miliyan 6

Kamfanin sada zumunta na LinkedIn ya amince ya biya diyyar dala miliyan shida bayan da hukumar kwadago ta Amurka ta gano cewa ya gaza samar da cikakken bayani game da yawan sa'oi da maikatansa kan shafe suna aiki.

Kamfanin zai biya dala miliyan 3.5 a matsayin kudin da be biya ma'aikatansa ba da kuma diyar dala miliyan 2.5 zuwa ga ma'aikatansa 359 ciki har da tsofaffin ma'aikata.

Ya amince ya rika samar da horaswa tare kuma da raraba tsare tsarensa akan ma'aikata da ba sa barin ofis akan lokaci.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin LinkedIn

LinkedIn ya ce zai cigaba da ba gwaninta fifiko kuma ya kosa ya yi gyra domin shawo kan lamarin.

Mataimakiyar shugaban kamfanin Shannon Stubo ta ce rashin isasun ma'aikata da zasu sa ido akan sa'oi da ma'aikata kan shafe suna aiki, shi ne ya janyo haka .

Hukumar kwadago ta Amurka ta ce ma'aikatan da lamarin ya shafa na aiki ne a California da Illinois da Nebraska da kuma Newyork.

Hakkin mallakar hoto Getty

Susana Blanco wadda jami'a ce a hukumar kwadago ta ce tsarin na kawo illa ga ma'aikata, kuma ba a biyansu kudin da ya kamata kuma ba sa ba iyalansu kulawar da ta kamata

Sai dai hukumar kwadago ta ce kamfanin LinkenIn ya kare mutuncinsa saboda ya bada hadin kai a binciken da aka yi kuma ya ce zai dauki kwararan matakai domin kaucema aukuwar hakan nan gaba.

David Well daga hukumar tsara albashi da lokutan aiki ya ce kamfanin ya nuna dattaku kuma ya bada hadin kai ga ba masu bincike

Ya kuma ce sun ji dadin shawarar da kamfanin LinkedIn ya yanke wajen daukar matakan da zasu tabbatar ana bin kaidojin da suka da ce.