Nigeria za ta binciki rahoton Amnesty

Image caption Sojin sun ce manufar kawo karshen ta'addanci a Nigeria ita ce ta hanyar murkushe duk wasu miyagun ayyuka.

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin keta hakkin bil adama da kungiyar Amnesty International ta yi wa dakarun kasar.

A wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun Kakinta Manjo Janar Chris Olukolade, ta ce za su dauki wannan batu da muhimmanci.

Ta kuma kara da cewa sun damu matuka da hotunan bidiyon da ake ta yadawa wadanda suka zama hujja ga kungiyar ta Amnesty.

Haka kuma rundunar sojin ta ce baya ga binciken hadin guiwa ta kuma kafa wani ayarin manyan jami'an soja da kuma kwararru a fannin kimiyya domin nazarin hotunan bidiyon.

Sanarwar ta kuma nuna cewa duk wanda aka samu hannunsa a cikin wannan lamari zai fuskanci shari'a kamar yadda doka ta tanada.

Karin bayani